Rikici Ya Barke Sakamakon Kalaman Suka Da Mawaƙi Rarara Yayi Ga Buhari

FB IMG 1698531586245

Kalaman suka da mawaki Dauda Kahutu Rarara yayi ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari sun haifar da zazzafar rik!ci a tsakanin wani masoyin Buhari da masoyin mawaki Rarara a jihar Kaduna.

Alfijir Labarai ta rawaito tun da fari dai, wani masoyin Buhari mai suna Mika’ilu Shehu Idris ne ya zag! mawaki Rarara a sakamakon sukar da Rarara ya yiwa tsohon shugaban kasa Buhari a wani taron manema labarai da Rarara ya gabatar a wannan mako.

Lamarin da bai yiwa masoyin mawaki Rarara Aliyu Hashimu dadi ba, kuma rikici ta barke a tsakanin masoyin Buhari da masoyin mawaki Rarara, inda masoyin Rarara wato Aliyu Hashimu ya lakadawa masoyin Buhari wato Mika’ilu Shehu Idris dukan kawo wuka.

Shedun gani da ido, sun tabbatar da cewa sun yi iya kokarin su don sasanta rikic!n amma lamarin ya ci tura har sai da masoyin Mawaki Rarara wato Aliyu Hashimu ya bawa masoyin Buhari kashi.

Yanzu haka dai masoyin Buhari wato Mika’ilu Shehu Idris, ya garzaya babbar kotun shari’a dake Kawo a jihar Kaduna don neman hakkin sa, bisa dukan kawo wuka da Aliyu Hashimu masoyin Rarara yayi masa a gaban jama’a.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

One Reply to “Rikici Ya Barke Sakamakon Kalaman Suka Da Mawaƙi Rarara Yayi Ga Buhari”

  1. Ikon Allah! Wahallalun banza abinda Rarara yafada ai gaskiyache Buhari yagurguza kasa Yakuma butulchewa talakan Nigeria don Rarara yabutulche masa menene laifi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *