Gwamna ya ce an ware kimanin Naira biliyan 6 domin biyan ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya kimanin 5,500 hakkokin su.
Alfijir Labarai ta rawaito Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai ranar Asabar a Jihar.
Abba ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda gwamnatin da ta shude ta gaza biyan yan fansho hakkokin wanda ya kai sama da Naira biliyan 40.
Hakazalika Gwamnan ya yi alkawarin biyan dukkanin wadanda suka gama aikin hakkokin su cikin Shekarun biyu masu zuwa.
An cimma matsayar ne a taron majalisar zartarwa na mako-mako a ranar Laraba. In Ji Gwamnan.
Ya kara da cewar wadanda za su ci gajiyar kudaden da za’a biya za su kasance ne, wadanda suka yi ritaya a matakin albashi ma kasa-kasa, wadanda kudaden su ka Kai Naira miliyan daya zuwa kasa, inda ya jaddada cewa kudaden da za’a biya yan fanshon ba bashi aka karɓo su ba .
A yayin Jawabinsa gwamnan ya nuna damuwarsa da halin da ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya suke shiga a jihar, bayan hidima da suka yiwa kano, amma gwamnatin da ta shude ta ki biyansu hakkokinsu.
“Muna da jerin sunayen wadanda zasu amfana, kuma muna da kudaden a hannu, nan da mako mai zuwa za mu fara biyan ba tare da bata lokaci ba. In Ji Gwamnan.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp