Ronaldo ya bada Otal dinsa dake Marroco Kyauta don samar da matsuguni ga waɗanda girgiza ta shafa

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr ta kasar Saudi Arabia Cristiano Ronaldo ya bayar da hotel dinsa Mai suna Pestana CR7 dake birnin Marrakesh na kasar Morocco a matsayin matsuguni ga wadan da girgizar kasa ta rutsa dasu a kasar Morocco.

Alfijir Labarai ta rawaito bayan Ibtila’in girgizar kasa da ya afku a Marroco Ɗan wasan Portugal da Al-Nassr Cristiano Ronaldo wanda duk wani abu na Iftila’i ko makamancin haka ya faru ya kan bayar da ko kyautar kudi ko kuma bayar da wata gudunmawa ta musamman to yanzu ma ya taka rawar gani.

Ronaldo da kansa ya wallafa wani sako a shafinsa na Twitter X na mika kyautar Otal din nasa ga wadanda Lamamin ya rutsa da su, wanda ke birnin Marrakesh din Morocco, a nan girgizar kasar ta faru.

To sai dai rahotanni sun bayyana Girgizar kasar ta yi kamari ne a wani yanki mai tsaunuka mai nisan kilomita 71 da garin Marakesh a cewar hukumar kula da binciken yanayin kasa ta Amurka.

Da misaflin karfe 23:11 na agogon kasar ne watau karfe (22:11 GMT) girgizar kasar ta faru.

An kuma sake samun girgiza kasa mai karfin maki 4.9 bayan mintuna 19.

An samu asarar rayuka a Marrakesh da garuruwa da dama a kudancin Kasar a cewar ma’aikatar cikin gida.

Shima dai dan wasan Morocco da PSG Achraf Hakimi, da abokan wasansa a kasar sun bayar da kyautar jini ga wadanda girgizar kasar ta faru.

Ya kuma mika sakon jaje ga wadanda wannan lamari ya shafa, ya kuma ce zai iya bakin kokarinsa domin bayar da gudunmawa ga wadanda girgizar kasar ta shafa.

Ko a baya ma dai irin wannan girgizar kasar ta taba rutsawa da ɗan wasan kasar Ghana Christian Atsu a kasar Turkiyya.

Kawo zuwa wannan Asabar din rahotanni sunce Girgizar-ƙasa ta kashe sama da mutum 1,037 a kasar ta Morocco.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *