Rundunar Soji ta kori Wata Soja bisa laifin sace kayan zinare da yakai kimar N35m.

IMG 20240524 WA0222

Daga Aminu Bala Madobi

An sallami wata sojar Najeriya daga aiki bayan da ta sace kayan adon zinare da aka ce sun kai Naira miliyan 35 daga hannun matar wani Janar din sojan da ta ke aiki da ita a jihar Kaduna.

Alfijir labarai ta rawaito a cewar wani bincike, matar sojan mai suna Lance Kofur Jonah Comfort mai lamba 15NA/74/4422F, ta aikata laifin ne a farkon watan Mayu.

Rahotanni sun ce ta shiga dakin uwargidan matar sojan ne ta sace kayan adon.

Daga bisani Sojar ta sayar da kayan adon ga wani mai sayar da kayan adon a Kaduna a kan Naira miliyan biyar.

Bayanai sun ce tuni hukumomin kasar suka ce lamarin ka iya haifar da cece-kuce a kan yadda matar babban hafsan ta samu kayan ado na miliyoyin Naira duk da kasancewarta uwar gida.

Majiyoyin da suka zanta da manema labarai sun ce jami’an ‘yan sandan suka kame mai kayan adon.

“Sojar macen ta dade tana sa ido a kan matar kafin ta sace kayan adon da kudinsu ya kai Naira miliyan 35 wanda daga baya ta sayar wa wani mai kayan adon Naira miliyan 5 amma abin takaici an kama ta.

“Abin takaici, yawancin wadannan sojoji mata matan manyan jami’anmu sun mayar da su bayi. Yanzu an sallame ta, an saka ta a gidan jarun.”

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da hukumomin sojin kasar suka kori wasu sojoji uku da ‘yan sanda suka kama da laifin fashi da makami da garkuwa da mutane.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/F9mRRuOf58G3MlLKsNCJbL

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *