Rundunar Sojin Najeriya Ta Tura Dakaru 177 Guinea Bissau Don Wanzar Da Zaman Lafiya A Kasar

FB IMG 1719484328567

Rundunar Sojin Najeriya ta aike da dakaru 177 zuwa ƙasar Guinea Bissau don taimakawa wajen maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar da ke yammacin Afirka.

Alfijir labarai ta ruwaito shugaban sashen gudanarwa na rundunar sojin ƙasa ta Najeriya, Manjo Janar Boniface Sinjen, ne ya bayyana haka ranar Laraba lokacin bikin yaye sabbin sojojin musamman na tallafa wa ayyukan ƙungiyar Ecowas a cibiyar horas da sojoji ta Jaji da ke Kaduna.

Yayin da yake jawabi ga dakarun kafin tafiyarsu zuwa Guinea-Bissau, Manjo Janar Sinjen, ya ce ƙasar – wadda ke yammacin Afirka na fama da matsalolin shugabanci, lamarin da ka iya haifar da barazana ga zaman lafiyar yankin yammcin Afirka.

Ya ƙara da cewa aika dakarun zuwa Guinea-Bissau da gwamnatin ƙasar ta yi ta hanyar ƙungiyar Ecowas ya nuna irin goyon bayan ga Najeriya ke bai wa Ƙasar Guinea-Bissau domin maido da ƙimarta, tare da magance matsalolin da ta fuskanta da kuma ƙarfafa dimokraɗiyyarta da kuma wanzar da zaman lafiyar ƙasar.

“Ya ku mazajen sojoji, an ba ku cikakken horo a wannan gida domin taka wannan muhimmiyar rawa”.

“Ina umartar ku, da ku zama jajirtattun dakaru wajen wannan gagarumin aiki na wanzar da zaman lafiya, ƙarƙashin inuwar Ecowas. Za ku yi aiki ne a ƙasar da ke fama da rƙicin ƙabilanci, don haka sai kun jajirce”, in ji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *