Alfijr ta rawaito rundunar sojin saman Najeriya ta fara shirin daukar sabbin ma’aikata na sojojin sama ga ƴan Najeriya masu mafi ƙarancin karatu.
Hukumar kan haka ta shawarci ‘yan Najeriya da su nemi guraben aikin yadda ya kamata kafin karewar wa’adin.
Rundunar sojin saman Najeriya ta sanar da cewa masu bukatar aikin bayan tsallake matakin horon da sojoji zasuyi za a kara musu girma zuwa matsayin jami’in tsaro.
Rahotanni sun rundunar ta kuma samar da hanyoyin tuntuɓar masu ruwa da tsaki dake daukar ma’aikata ta Najeriya ta imel: careers@airforce.mil.ng ko kuma ku kira layukan tallafin su a ranakun mako.
Hukumar tace masu neman aikin dole ne su mallaki mafi ƙarancin cancantar digiri me daraja ta biyu ko kuma babban daraja daga manyan Jami’o’i da sauran manyan makarantu. Haka kuma masu neman aikin ya zama wajibin su gabatar da takardar shaidar kammala NYSC.
Masu sha’awar neman aikin kuma dole ne su kasance ‘yan Najeriya, marasa aure kuma dole ne su kasance tsakanin shekaru 20 zuwa 30.
Rundunar ta kuma ce za ta dauki matasa mata masu karatun sakandire da karamar diploma har ma da masu NCE masu karancin shekaru daga 18 zuwa 25
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
I like this work so much
Please help me I want join you
You impressed