Rundunar Yan Sandan Jihar Kano ta Bayyana Cewa ta kama Mamallakin Gini Mai Hawa Biyu Da ya rufta a Unguwar Kuntau Dake Karamar Hukumar Gwale
Alfijir Labarai ta rawaito cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar Yan Sandan Jihar Kano SP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya aikewa Ammasco Radio yace, Tuni rundunar ta Fara Gudanar da bincike Kuma da zarar ta Kammala zata Gurfanar da Mamallakin Ginin gaban kotu
Rundunar Yan Sandan tace Zatayi aiki Ka fada da ka fada da Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano Domin Cigaba da Gudanar da bincike akan yadda aka Gaza bin Ka’idojon da suka Kamata Wajen Gudanar da Ginin
A ranar juma’a ne dai Wani Gini a Unguwar Kuntau ya rufta, Wanda Yayi Sanadiyar Mutuwar Mutane uku Yayinda wasu Mutum Biyar suka jikkata
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk