Rundunar Yan Sandan Katsina Ta Sanya Miliyan 50 Ga Duk Wanda Ya Bayyana Yadda Za a Kama Wasu Yan Bindiga 2

FB IMG 1709485484086

Rundunar yan sandan jihar Katsina ta sanya kyautar naira miliyan hamsin, ga duk wanda ya taimaka wa yan sandan da wani labari na inda za a gano wasu manyan yan bindiga biyu da suka addabi jihar Katsina don kamo su.

Alfijir labarai ta rawaito kakakin rundunar yan sandan jihar Katsina ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana sunayen yan bindigar da Modi Modi da kuma Jan Kare, da suka fitini yankin Kankara da Safana dake cikin jihar Katsina

Rundunar ta kara da cewa duk wanda ya sami labarin inda yan bindigar suke, da ya garzaya kai tsaye zuwa shalkwatar yan sandan dake Katsina don kai masu ruhuto, ko a kira su ta wadannan lambobin 07015142112 08023871144,”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *