Sakon ATIKU ga ‘yan Najeriya Kan bikin ranar ‘yancin Kai karo na 63

FB IMG 1696100553865

Bikin na ranar yancin Kai a bana yazo lokacin da kasar mu ke kan Wani kadami Mai muhimmanci game da batun makomar ta a fannonin rayuwar mu daban-daban.

Shekaru 63 da suka Gabata, lokacin da kasar nan ta samu yancin Kai, ta kasance kan kyakkyawan tsari na adalci da kyakkyawan yanayi.

A Matsayin mu na kasa, mun ci gaba da kokarin aiwatar da burikan iyayen wannan kasa na ci gaba da tabbatar da adalcin zamantakewa.

Mun taba tsintar kan mu cikin yanayin da kasar mu ta Yi suna a duniya ta hanyar fitattun ‘yan wasan mu Maza da mata, da bajintar da malaman mu ke nunuwa a fannin Ilimi da baje kolin basirar da mutanen mu ke nunawa a fagen wakoki.

Haka Kuma, irin bajinta da hazakar da matasan wannan kasa ke nunawa Kuma suka ki yarda a kashe masu gwiwa, abin karfafa gwiwa ne da alfahari yayin da muke murna a yau.

Kuzari da karfin jikin da matasan Najeriya ke da shi, shi ne babban Ginshiki na Samar da ma’aikata da kwarewar da ake bukata wajen Gina tattalin arziki a duniya.

A dukkan fadin duniya, Kuma a dukkan fannonin rayuwar Dan Adam, matasan Najeriya sun nuna cewar suna da kwarewar da zasu goga kafada da takwarorin su ko Ina cikin duniya.

Waccan nasara da matasan kasar nan suka samu, shi ne kashin bayan abinda ya bamu damar wannan biki a yau.

Saboda haka, ni a wuri na, kalubalen Dake gaban mu gaba Daya shi ne tabbatar da ganin cewar wadanda ke shugabancin wannan kasa da ta kasance gida a wurin mu, sun cancanta don alfaharin mu ba wadanda zamu ji kunya ba.

Dimukuradiyyar mu ta bunkasa saboda amincewar mu da cewar idan aka tsara ta yadda ya kamata zamu amfana mu Kuma amfanar.

A Matsayin mu na ‘yan Najeriya, dukkan mu sheda ne kan halin matsin rayuwa da ake ciki da matsalar tsaro da sauran fannonin rayuwa da suka shiga Wani hali.

Yayin da nake kiran mu da mu dogara ga ALLAH mahaliccin mu, wajibi ne mu shirya domin Bada gudummawa don kubutar da kasar nan daga halin rashin tabbas zuwa ga kwanciyar hankali.

Ina Taya murna ga ‘yan uwana ‘yan Najeriya ciki harda abokai na kasar mu a ciki da wajen ta, Ina taya ku murnar wannan Rana ta samun yancin Kai.

Allah Ya Yi muku albarka, Allah Kuma Ya albarkaci Tarayyar Najeriya.

Atiku Abubakar
Wazirin Adamawa
Tsohon mataimakin shugaban kasa 1999 zuwa 2007
Kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023.
Abuja 30 Ga Satumba, 2023.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

One Reply to “Sakon ATIKU ga ‘yan Najeriya Kan bikin ranar ‘yancin Kai karo na 63”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *