Sakon Kwankwasiyya Ga Kafatanin Al’ummar Jihar Kano – Hon Sagir Koki

Alfijr ta rawaito sabon wakilin karamar hukumomin Kano municipal a majalisar wakilai ta kasa, Kuma Jigo a Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano Hon injiniya Sagir Ibrahim koki ya aike da sakon taya Murna ga Sabon Zababban Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf.

Hon koki Cikin Sanarwa da ya fitar a wannan rana ta talata ta Hannun Nazifi Bala Dukawa Hadiminsa na Musamman kan harkokin Yada Labarai ta yabawa Al’ummar Jihar Kanon bisa tsayawa tsayin daka da sukayi suka zabi Abba Kabir Yusuf suka kuma yi ta Addu’a har sai da nasarar ta tabbata.

Dan majalisar Wanda shine jagoran ilimi da matasa a Municipal yace zabin Abba Gida Gida da Mutanen Kano suka yi zai samar da gagarumin sauyi a gwamnati da siyasar Jihar Kano, a cewar sa gwamnati ce za’ayi ta Al’umma wacce zata zama gatan talaka..

A cewar sa suna da yakinin Sabon Gwamnan na Kano zai mayarda hankali sosai a fannin Inganta Ilmi, kula da lafiya,Kasuwanci, Noma da sauran Abubuwan bunkasa rayuwar Al’umma.

Hon sagir koki yayi amfani da wannan dama wajen Mika sakon taya Murnar sa ga Madugun Darikar Kwankwasiyya Dr Rabi’u Musa Kwankwaso da Kuma Sabon Gwamnan na Kano Engr Abba Kabir Yusuf a madadin iyalansa da ‘yan Uwa da Kuma daukacin Al’ummar mazabarsa ta kano municipal

Kamar yadda Nazifi Bala dukawa hadimi na musamman kan yaÉ—a labarai ya fitar a yau Talata.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *