Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya jaddada cewa gwamnoni na karkatar da kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke bai wa ƙananan hukumomi suna sha’anin gaban kan su da kuɗaɗen.
Alfijir labarai ta ruwaito Sanata Barau ya bayyana haka a ranar Laraba, yayin da ya shugabanci zaman majalisar dattawa.
Ya furta haka ne bayan Sanata Kawu Sumaila na NNPP daga Kano ya kawo ƙorafin buƙatar a bai wa kowace ƙaramar hukuma cin gashin kanta.
Sanata Jibrin ya ce tabbas wasu gwamnoni su na yiwa ƙananan hukumomi illa sosai, saboda son zuciyar su.
Ya ce gwamnoni su na kamfatar kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke bai wa ƙananan hukumomi, lamarin da Barau ya ce zamba ce.
“Tsarin ƙananan hukumomi ya mutu murus, saboda kuɗaɗen da tarayya ke ba su, akasari duk gwamnoni ke karkatar da su.
“Za a ce ku je ku rubuto kuɗaɗen da ku ke buƙata, daga nan sai gwamna ya daddatsa kuɗaɗen ya kamfaci iya son ran sa.”
Amma fa ban ce haka dukkan gwamnoni ke yi ba. Akwai gwamnoni mutanen kirki, waɗanda ba su yin hakan. Amma wasu da na aikata hakan.” Cewar Barau.
Ya ce hanyar da za a iya bai wa ƙananan hukumomi cin gashin kan su. Hakan kuwa ba zai yiwu ba sai an shigar da dokar cikin Kundin Dokokin Najeriya.
Daga nan ya jinjina wa gwamnonin da ba su cirar kuɗaɗe daga asusun ƙananan hukumomi, sannan ya yi kira gwamnonin da ke cirar kuɗaɗen su daina.
Sahara Reporters
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl