Sarki Aminu bai taba zama Sarkin Kano ba, face Sarkin ƙwaryar garin – In ji Gwamnatin Kano

FB IMG 1716907390129

Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna Abba Kabir Yusuf Sanusi Bature ya bayyana cewa Aminu Ado Bayero bai taba zama Sarkin Kano ba.

Alfijir labarai ta ruwaito Bature ya ce tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya naɗa Aminu Ado Bayero a matsayin sarkin kananan hukumomi takwas na birnin Kano.

Da yake magana a gidan Talabijin na Arise, Bature ya ce Ganduje ya naɗa Bayero Sarkin Kano ne saboda batanci ga masarautar.

A cewar Bature Ganduje ya shigo da siyasa ne a Masarautar Kano saboda wani ra’ayin kansa.

Ya ce, “Aikin da Gwamnan na yanzu ya yi shi ne kare martabar masarautar a matsayinta na babbar Masarauta a Najeriya kafin daga bisani Najeriya da kundin tsarin mulkin kasar ta sauya tsarin da ya shafe shekaru sama da dubu inda mutane ke rayuwa tare a karkashin Sarki daya.

Gwamnatin Ganduje da ta shude ta yanke shawarar bata wannan tarihin inda ta shigo da siyasa a ciki.

Siyasantarwar da akayi wa Masarautar shi ne abin da Gwamna Yusuf ya yi alkawarin dawo da martabar da aka rasa a Gwamnatin baya. Kuma wannan dai ba shi ne karon farko da aka tsige Sarki ba. Ganduje ya tsige Sanusi inda ya bar Kano domin a samu zaman lafiya, a yanzu kuma Sanusi ya koma bayan soke dokar da ta tsige shi.

Ina so in bayyana cewa Aminu Ado Bayero bai taba zama Sarkin Kano ba, an naɗa shi ne Sarkin Kananan Hukumomi takwas na birnin Kano.

Don haka da aka yi wa dokar kwaskwarima, Masarautar da Aminu ya yi aiki ba ta wanzu ba a yanzu domin dokar Masarautar ta 2019 ta lalata babbar masarautar.

Shi ne Sarkin Kano 14, amma ba wai ana nufin ikonsa na kananan hukumomi 44 na Kano ba ne, kawai na kananan hukumomi takwas ne da ke cikin gari.

Gwamna Yusuf ya tsige Aminu Ado Bayero ne a lokacin da ya maido Muhammad Sanusi a matsayin Sarkin Kano.

Duk da matakin da Gwamna ya ɗauka, Aminu Ado Bayero ya ki barin fadar sa ta Nassarawa.

Tun daga lokacin ne Bayero ya ki amincewa da matakin da Gwamnatin Jihar ta dauka inda ya ƙalubalence ta a gaban kotu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *