Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero Yayi Sabbin Naɗe-Naɗe

Mai Martaba ya hori wadanda aka nada din da su zama masu gaskiya da rikon amana tare da jajircewa a ayyukansu.

Alfijir Labarai ta rawaito mai martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero CFR CNOL JP ya amince da naɗin sabbin wakilai a kasuwar Kwari, kasuwar Singa da kuma kasuwar Wafa a yau Litinin.

Mai Martaba ya bayyana wadannan Naɗe-Naɗen ne dan samun wakilnchin masaurauta a cikin kasuwanan na jihar kano.

Waɗanda aka Naɗa din sun hada da :-

  1. Alh Bashir Dan Bako ( Wamban Wafa )
    Wakilin sarkin kano A Kasuwar Wafa
  2. Alh Aminu A Mai sunan Sarkin
    Wakilin sarkin kano a Kantin Kwari
  3. Alh. Isah Abba . Wakilin sarkin kano A Kasuwar Singa

Mai Martaba ya hori wadanda aka nada din da su zama masu gaskiya da rikon amana tare da jajircewa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *