Sarkin kano Aminu Ya Taya Gwamna Abba Kabir Yusuf Murnar Ranar Arafat Da Kuma Bikin Sallah.

FB IMG 1716824436390

Sarkin ya kuma mika sakon taya murna ga shugaban kasa Bola Tinubu, inda ya bukaci shugabannin biyu da su ci gaba da aiwatar da ayyukan raya kasa masu ma’ana don rage wa ‘yan kasa wahalhalun tattalin arziki da suke fuskanta a halin yanzu.

Alfijir labarai ta ruwaito a wani jawabi na musamman, Sarkin ya yabawa Gwamnatin Kano da Gwamnatin tarayya bisa ƙoƙarin da suke yi na wanzar da zaman lafiya da gudanar da ayyukan raya kasa.

Ya godewa jami’an tsaro bisa tabbatar da zaman lafiya a cikin abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, ya kuma bukace su da su ci gaba da ƙoƙarin Ganin Kano ta zauna lafiya.

Ya ci gaba da cewa, “A matsayina na dan kasa mai bin doka da oda, ina bin umurnin da jami’an tsaro suka bayar na jingine shirin da muka yi a baya na gudanar da Hawan Nassarawa da Dubar na Gargajiya, domin ganin kowa ya ci gaba da gudanar da harkokinsa ba tare da fargabar tsangwama ko kai hari ba. “

Sarkin Kano na 15 ya shawarci jami’an tsaro da su tabbatar da tsaron mutanen Kano tare da hana duk wani abu da ya shafi kowa. Ya kuma ja hankalin al’ummar Kano da su marawa gwamnatinsu baya ta hanyar yin biyayya ga shirye-shiryenta da manufofinta domin a samu ci gaba tare da ƙasa baki daya.

Da yake jawabi a wajen watsa shirye-shiryen na musamman, Sarkin Dawaki Babba Aminu Babba DanAgundi ya sanar da cewa, Sarkin ya umarce shi da ya sanar da matakinsa na yin Sallah a filin Idi na da yake Nassarawa. “Sarki a matsayinsa na mutum mai mutuntawa kuma mai mutunta doka, ba wai kawai ya nemi mu sanar da dakatar da shirin yin sallar idi a filin Idi ba, har ma ya amince ya yi sallah a fadar Nassarawa tare da talakawansa. Inji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *