Sarkin Kano Ya Daga Likkafar Wasu Hakimai Da Naɗa Sabbin Sarautu

Alfijr ta rawaito Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP, CNOL, Ya sake nada wasu sababbi Hakimai guda hudu tare da daga Darajar wasu Hakimansa guda shida.

Da yake jawabi lokacin da aka nada Hakiman, Mai Martaba Sakin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, yace an nadasu ne bisa cancantar su da irin gudunmawar da suke bayarwa a cikin al’umma.

Wadanda aka nada din sun hadar da Alhaji Nura Sunusi a Matsayin Dan Darman Kano da Alhaji Sarki Hamidu Bayero a Matsayin Barayan Kano da Alhaji Sayyadi Muhammad Yola a matsayin Fagacin Kano da kuma Alhaji Bello Idi a Matsayin Kaigaman Kano.

Sai kuma Hakiman da aka ciyar dasu gaba sun hada da Malam Umar Sunusi Bunun Kano ya koma Dan Makwayyon Kano da Malam Ibrahim Hamza Bayero Dan Madamin Kano zuwa Dan Ruwatan Kano da Malam Lamido Abubakar Bayero Yariman Kano inda ya zama Bunun Kano.

Saura Hakiman da aka ciyar dasu gaba sune Alhaji Aminu Ahmad Sadiq Zamnan Kano zuwa Dan Madanin Kano da Alhaji Magaji Galadima Kachallan Kano zuwa Magayakin Kano da kuma Alhaji Bello Habibu Dankadai Fagacin Kano zuwa katikan Kano.

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR JP, ya bukaci hakiman da aka nada su zamo jakadu nagari a duk inda suka samu kansu tare da gudanar da aikinsu da gaskiya da amana tare da Sanya tsoron Allah.

Kamar yadda Abubakar Balarabe Kofar Naisa Babban Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano
Ya sanyawa hannu

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

One Reply to “Sarkin Kano Ya Daga Likkafar Wasu Hakimai Da Naɗa Sabbin Sarautu”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *