Mai martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayaro yayi kira ga Shugaban sojojin sama na Nigeria yayi kokari wajen dawo da Makarantar sijojin sama dake garin kwa a yanki Karamar Hukumar Dawakin Tofa wadda aka rufe sakamakon rashin tsaro a watannin baya.

Alfijir Labarai ta rawaito mai Martaba Sarkin yayi wannan Kira ne lokacin da shugaban sojojin Sama na Nigeria ya ziyarceshi a fadarsa.
Sarkin ya kara da cewa makarantar tana da muhimmanci ga Al umar jahar kano da Arewacin Nigeria baki daya.
Daga nan mai martaba ya taya Shugaban Sojojin Sama (Chief of Air Staff) murnar samun wannan matsayi na shugabancin sijojin sama na Najeriya baki daya, inda yayi fatan matsayin nasa zai taimaki Al umar kano da Arewa da kasa baki daya.
Da yake nasa jawabin Shugaban sojojin saman Hassan Bala Abubakar ya bayyanawa Mai Martaba sarkin cewa Amatsayinsa na dan Asalin jahar kano ya zone ya gabatarda kansa da kuma matsayin da ya samu Sannan su nemin Hadin kan masarautar kano wajen Tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kasa baki daya.
A lolacin ziyarar Shugaban Sojojin yana tare da shugaban rundunar sojojun sama dake nan kano.
Sa hannu.
Abubakar Balarabe Kofar Na I said
Sakataren yada Labarai na Masarautar Kano.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk