Sarkin Kwallo Pele Ya Mayar Da Martani Ga Cristiano Ronaldo

Alfijr ta rawaito Shahararren dan wasan Brazil, Pele, ya gode wa kyaftin din Portugal Cristiano Ronaldo da ya yi masa kyawawan kalamai da fatan alheri.

Sarkin kallon kafa wanda yanzu yake da shekaru 82, a halin yanzu yana murmurewa a asibitin Albert Einstein da ke Sao Paulo bayan da aka daina saka rai a kansa, saboda yanayin da cutar sankara ta maida shi, yana mai da martani ne ga kalaman Ronaldo a Instagram, bayan fara murmurewa.

A ranar Lahadi ne aka jiyo Ronaldo ya ce ba zai taba juya wa abokan aikinsa baya da kasarsa baya ba.

Dan wasan mai shekaru 37 ya bayyana hakan ne a wani dogon rubutu da ya wallafa ta shafinsa na Instagram bayan fitar da Portugal daga gasar cin kofin duniya ta 2022 a ranar Asabar.

Dan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar ya kasa ceto Portugal, bayan da suka yi rashin nasara a hannun Morocco da ci 1-0 a gasar cin kofin duniya a karshen mako.

Ronaldo ya ce a cikin wani dogon sako da ya yi, “Na yi fafutuka ne a gasar cin kofin duniya.

Na kuma yi yaƙi sosai don wannan mafarkin.

A cikin wasanni 5, na zira kwallaye a gasar cin kofin duniya sama da shekaru 16, koyaushe ina tare da manyan ‘yan wasa da goyon bayan miliyoyin Portuguese, na ba da komai.

Ban taba mayar da fuskata wajen fada ba kuma ban yi kasa a gwiwa ba kan wannan mafarkin.”

“Abin baƙin ciki, jiya mafarkin ya ƙare.

Ina son ku duka ku sani cewa an faɗi abubuwa da yawa, an rubuta da yawa, an yi hasashe da yawa, amma sadaukar da kaina ga Portugal bai canza ba na ɗan lokaci.

A koyaushe ina gwagwarmaya don manufar kowa, kuma ba zan taba juya baya ga abokan aikina da kasata ba.”

[07/12, 11:35 pm] Musa Best Seller: Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

One Reply to “Sarkin Kwallo Pele Ya Mayar Da Martani Ga Cristiano Ronaldo”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *