Sarkin Musulunci Ya Magantu Akan Gida Katafaren Masallaci Da A Y Mai Kifi Yayi A Kano

FB IMG 1709915862508

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji sa’ad Abubakar III ya yabawa dan kasuwar nan Alhaji Adamu Yahaya bisa gina katafaran masallacin juma’a da ya gina a unguwar kundila dan cigaban addinin musulunci.

Alfijir labarai ta rawaito Mai alfarmar sarkin musulmin ya bayyana haka ne a yayin gudanar da sallar juma’a data gudana a masallacin Bini Usman dake karamar hukumar Tarauni.

Alhaji Sa’ad Abubakar yace wannan masallaci yana daya daga cikin masallatai da kayiwa gini na zamani a don haka ne sai ya bukaci al’ummar dake yankin masallacin dasu kula da tsaftar masallacin .

A nasa jawabin mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya godewa dukkanin Wanda suka taimaka wajen gina masallacin musamman Wanda ya gina masallacin Adamu Yahaya Mai Kifi.

Mai martaba sarkin ya kuma kira da mawadata dasu yi koyi da irin wannan hali na bunkasa addinin musulci.

A nasa bangaren Alhaji Adamu Yahaya Mai Kifi yace wannan masallaci ya sadaukar dashi ne ga al’ummar musulmi baki daya baya daya daga cikin daga cikin gadonsa

Gwamnan jihar kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Kwamaren Aminu Abdulsalam Abubakar na daya daga cikin wanda suka halarci sallar ta juma’a a masallacin dake kundila a karamar hukumar Tarauni.

Kamar yadda Abubakar Balarabe Kofar Naisa Baban Sakataren yada labarai na Masarautar Kano ya sanyawa hannu.

FB IMG 1709915895528
Bude masallacin Bin usman A Y Mai kifi
FB IMG 1709915889182
Bude masallacin Bin usman A Y Mai kifi

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *