Alfijr ta rawaito wasu ƴan Najeriya su biyar na cikin wasu mutum 11 da jami’an Hukumar Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi ta Saudiyya suka kama da hodar Iblis a Jidda.
Hukumar da ta ke yaƙi da miyagun kwayoyi ta ƙasar ta ce gungun wadanda ake zargin sun boye hodar Iblis ɗin ne a wurare daban-daban domin kawar da hankalin jami’an tsaron ƙasar

Manjo Marwan al-Hazmi, wanda shi ne kakakin shugaban hukumar, ya ce dubunsu ta cika a wani simame da jami’an hukumar suka kai musu.
Kamfanin dillancin labaran Saudiyya (SPA) ta ce ’yan Najeriyar da aka kama, suna da takardun ziyarar kasar ne, wasu mutum huɗu kuma mazauna a ƙasar ne, sauran biyun kuma baƙin haure ne da suka shiga ƙasar ta ɓarauniyar hanya.

Saudiyya dai na da tsauraran dokoki a kan ta’ammali da miyagun kwayoyi, inda ake yankewa masu fasakwaurinsa hukuncin kisa.
Dillalansa da masu amfani da shi kuma akan ɗaure su a gidan yari ko a karɓi tara a wajen su mai tsananin gaske ko kuma a kore su daga kasar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Alfijr Labarai YouTube. Best Seller ChannelTwitter. @MusabestsellerInstagram. @musa_bestsellerKo a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ