Saudiyya Ta Samu Nasarar Raba Wasu Jarirai Ƴan Tagwaye Daga Najeriya 

Alfijr ta rawaito wasu gungun likitocin kasar Saudiyya, a ranar Alhamis, ta yi nasarar raba wasu tagwayen ‘yan Najeriya Hassana da Hassina.

Nasarar na zuwa ne bayan shafe sa’o’i 14 ana aikin raba su a Birnin Riyadh na kasar Saudiyya.

Likitocin tun da farko sun bayyana cewa tagwayen suna cikin koshin lafiya a asibitin kwararru na Sarki Abdullah.

Tagwayen maza ne, wadanda aka haifa a Kaduna a ranar 12 ga watan Janairun shekarar 2022, sun yi tarayya a cikin ciki, ta abubuwa da dama da suka haɗar da Mazaunai, hanta, hanji, da wajen fitsari.

Gungun Likitocin da ke da mambobi 85 da suka hada da kwararrun likitocin tiyata 35 da kuma ma’aikatan jinya da fasaha suna karkashin jagorancin Dr. Abdullah Al-Rabeah.

Kafin a fara aikin, Al-Rabeeah ya ce aikin zai kunshi matakai takwas.

An yi aikin tiyatar ne bisa umarnin Sarki Salman na Saudiyya.

A baya dai ayyukan jin kai na Saudiyya sun taimaka da wasu tagwaye guda 130 daga kasashe 23 a tsawon shekaru 33, kuma Hassana da Hassina za su kasance tagwaye na 56 da aka raba a karkashin hakan.

Jakadan Najeriya a kasar Saudiyya Yahaya Lawal ya ce godewa kasar bisa wannan kokari da suka yi musu, a madadin yan Najeriya da gwamnatin kasar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *