
Alfijr ta rawaito Zababben Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya shawarci ɗaiɗaikun mutane da kungiyoyi masu gine-gine a filayen gwamnatin jihar da su dakata nan take.

Sanarwar na kunshe ne cikin wani sako da ya wallafa safiyar Juma’a a shafinsa na Facebook.

A cewarsa, “kamar yadda muka kudiri aniyar dawo da tsarin birnin Kano, ina shawartar jama’a da su daina duk wani aikin gine-gine a filayen gwamnati, a ciki da wajen makarantu.
“Wuraren addini da na al’adu, da dukkan asibitoci, da makarbarta, da kume gefen katangar birnin Jihar Kano ganuwa. ”

Haka kuma, a kunshin sanarwar da mai magana da yawun zababben gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar, an kuma shawarci dakatar da rushewa ko kuma ci gaba da aikin duk wasu gine-gine a filayen gwamnatin jihar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇