Sheikh Gumi Yayi Bayanin Yadda Ta Kasance A Tattaunawarsu da jami’an Tsaro

FB IMG 1711470490126

Sheikh Dr. Ahmad Gumi, ya ce ya tattauna da jami’an tsaron Najeriya da suka gayyace shi kan harkokin da suka shafi tsaro.

Alfijir labarai ta rawaito Dr. Gumi, ya amsa gayyatar da jami’an tsaro suka yi masa a ranar Litinin din da ta gabata a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook, ya ce shi bai fi karfin doka ba amma wadanda ba su da laifi ne kadai ke kan doka.

Ya ce babu wani abin fargaba a gayyatar da akai masa, inda yace ya tattauna da jami’an tsaron yadda ya kamata.

“A daren jiya na samu kiraye-kiraye da yawa daga masu mutane da ‘yan jarida kan gayyatar da jami’an tsaro suka yi min da kuma tambayoyi da suka yi min.

“Eh, mun sami kyakkyawar tattaunawa kan yadda za mu dakile ayyukan ta’addanci yayin da kowanne a fagensa ke kokarin don magance kalubalen tsaron da ke cutar da al’umma. Mun tattauna dasu ba tare da cin mutunci sai girmamawa.

“Dukkanmu muna bukatar a matsayinmu na al’umma mu hada kai mu yi aiki tare domin samun zaman lafiya mai dorewa. Na gode da damuwar da kuka nuna a gare ni. Allah ya ci gaba da tsare mu daga dukkan sharri. Amin,”Dr. Gumi ya rubuta bayan ganawa da jami’an tsaro.

Gumi akan ta’addanci

Dr. Ahmad Gumi ya sha yin suka kan yadda jami’an tsaro ke tafiyar da ayyukan ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma. Ya bayar da mafita ga rikicin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane da kuma yin garkuwa da jama’a domin neman kudin fansa.

Malam Gumi ya kuma soki yadda gwamnatin Najeriya ta wallafa sunayen mutanen da ta ke tuhuma a matsayin masu daukar nauyin ta’addanci. A ranar Larabar da ta gabata, gwamnatin Najeriya ta bayyana sunan daya daga cikin abokan Gumi, Tukur Mamu, tare da wasu mutane 14 a matsayin masu bada kudin ga yan ta’adda a Nigeria.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *