Shugaba Buhari Ya Umarci Cigaba Da Amfani Da Tsohuwar 200

Alfijr ta rawaito Shugaba Buhari ya bai wa babban bankin ƙasar CBN umurnin ya sake fito da tsofaffin takardun naira 200 domin a ci gaba da mu’amala da su a ƙasar.

Shugaban Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a cikin jawabin da ya yi wa al’ummar ƙasar da safiyar yau Alhamis.

Ya kara da cewar yana sane da irin halin wahala da al’ummar ƙasar ke ciki, ya ce za a ci gaba da amfani da takardar kuɗin ta naira 200 har zuwa 10 ga watan Afrilu.

Ya kuma buƙaci al’umma da su ƙara haƙuri kan halin da ake ciki.

Cikakken Bayani na nan tafe…

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

3 Replies to “Shugaba Buhari Ya Umarci Cigaba Da Amfani Da Tsohuwar 200

  1. YA KAMATA SHUGABA YA ZAMA ME KULAWA DA MASLAHAR ALUMMA GABA DAYA
    BA WAI YACE DOLE SAI TINANIN DA YAYI SHINE ALUMMA ZATA RAYUWA DASHI BA

  2. Alfinir muna jin dadin labaran da kuke feshe mu da su da dumi-dumi, da zarar sun faru,
    Aikin ku yana kyau. Ku ci gaba Allah ya taimaka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *