Shugaba Najeriya Tinubu Ya Zama Shugaban Kungiyar ECOWAS

Shugaban kasar Nigeria Bola Ahmed Tinubu ya zama sabon shugaban kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka wato ECOWAS.

Alfijir Labarai ta rawaito Tinubu na cewa “Za mu dauki demokradiyya da mahimmanci, Dimokuradiyya tana da matukar wahala amma ita ce mafi kyawun tsarin gwamnati,”.

Tinubu ya gaji Umaro Embalo na Guinea Bissau a matsayin shugaban kungiyar ta ECOWAS.

An sanar da nasarar Tinubu ne a taro kungiyar karo na 63 na shugabannin gwamnatocin kasashen ECOWAS.

Taron na kungiyar ECOWAS karo na 63 shi ne taro na farko da shugaban kasa Tinubu ya halarta a nahiyar Afirka tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

One Reply to “Shugaba Najeriya Tinubu Ya Zama Shugaban Kungiyar ECOWAS”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *