Shugaba Tinubu Yayi Sabbin Nade-Nade A Kasuwar Shinko Ta Kasa

FB IMG 1710375660100

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Mista Mairiga Aliyu Katuka a matsayin shugaban Hukumar kula da kasuwannin shinko na kasa.

Alfijir Labarai ta ruwaito wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar ta ce shugaban ya kuma nada Mista Emomotimi Agama a matsayin babban Darakta hukumar.

Frana Chukwuogor kuma an nada shi a matsayin Babban Kwamishinan kula da harkokin Shari’a.

Sai kuma Mista Bola Ajomale a matsayin Babban Kwamishinan kula da Ayyuka. Ita kuma Mrs. Samiya Hassan Usman a matsayin kwamishinar kula da harkokin hukumar.

Mista Lekan Belo kuwa a matsayin kwamishinan zartarwa. Da kuma Kasimu Garba Kurfi a matsayin Kwamishina.

Sanarwar ta kara da cewa, shugaba Tinibu ya bayyana kwarin gwiwar cewa dukkan mambobin hukumar za su yi amfani da kwarewarsu wajen ci gaba da aikin hukumar na samar da ingantacciyar kasuwa mai inganci, da gaskiya, ta yadda masu zuba jari za su samu kwarin gwiwa tare da bayar da gudummawa sosai ga harkokin kasuwanci. ci gaban tattalin arzikin kasa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *