Daga Aminu Bala Madobi
Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa hoton da aka kirkira dauke da hoton kansa sanye da kayan Paparoma.
Trump ya saka hoton a shafin sa na sada zumunta mai suna Truth Social a safiyar ranar Asabar.
Hoton, wanda ya tattara sama da masu kallo sama da 12,000, an sake dora hoton a fadar White House.
Hakan na zuwa ne bayan da shugaban ke kalaman barkwanci dake nuni da cewa yana son ya zama limamin coci.
Lokacin da aka tambaye shi wanda zai so ya gaji Paparoma Francis,. Shugaba Trump ya gayawa manema labarai a filin da ke fadar White House cewa: “Ina so in zama Paparoma. Wannan shine zabi na na daya.”
Trump ya ci gaba da cewa ba shi da wani fifiko da saura amma akwai wani Jagoran mabiya kiristanci wato Cardinal a New York wanda ya ke ganin zai iya zama Shugaban.
Izuwa yanzu haka ana ci gaba da gudanar da taron zaben sabon Fafaroma bayan mutuwar Fafaroma Francis, wanda ya rasu a ranar Ista litinin yana da shekaru 88 a duniya sakamakon bugun jini da bugun zuciya.
Bayyanar Donald Trump a jana’izar Paparoma Francis a makon da ya gabata sanye da riga shudi ta gargajiya ya jefa tambayoyi ga manazarta kuma an gan shi yana tauna abubuwa a bakin sa lokacin bikin.
Wasu masu suka kuma sun ce ganawar da Shugaba Trump ya yi a gefe da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky bai dace ba.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD