Shugaban Hukumar kula Da Asibitocin Jihar Kano Ya Kori Wasu Ma aikata Da Dakatar Da wasu

IMG 20231217 WA0136

Sakataren zartarwa na hukumar kula da asibitocin jihar Kano Dakta Mansur Mudi Nagoda ya amince da dakatar da jami’an tsaron asibitin haihuwa na Imamu Wali sannan ya umarci mahukuntan da su gaggauta debevwasu jami’an tsaron cikin gaggawa.

Alfijir labarai ta rawaito wannan na zuwa ne ya biyo bayan wani faifan bidiyo na wata mata mai nakuda wadda daga baya ta haihu a cikin mota sakamakon sakacin da jami’an tsaron ke yi na kulawa da marasa lafiya.

A cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafan sada zumunta, an gano wani mijin majinyacin ya yi ta kwankwasa kofar asibitin ba kakkautawa, amma jami’an tsaro ba a kowa cikinsu, wanda hakan ya sa mijin ya dauki hoton bidiyon faruwar ya kuma tura shi kafar sada zumunta.

Dokta Nagoda ya bayyana cewa, irin wannan lamari ya taba faruwa a ranar 26 ga watan Nuwamba, inda wata mata tana nakuda, kuma jami’an tsaron Nan ma basa nan, don haka sai mijin ya garzaya da ita asibitin kwararru na Murtala Muhammad. wanda shine mafi kusanci.

Hakazalika Dr Nagoda ya amince da dakatar da Wasu jami an gwaje gwaje su uku nan take, saboda laifukan da suka hada da sakaci, karbar kudi da kuma lalata da marasa lafiya musamman wadanda suke bukatar gwajin kuma basu da kudin biyan.

Ya bayyana cewa dakatarwar ta su ya zama dole kuma za a kafa kwamitin da zai gudanar da bincike, bin hanyoyin da suka dace, duk kuma wadanda ke da hannu a ciki za a dauki mataki kansa.

Dokta Nagoda ya koka da cewa HMB ba za ta kasance a bangaren tsaro a kowane lokaci ba, ya kuma yi gargadi mai karfi ga duk wanda ya ce, “Kada wanda ya isa ya zo wurina ko wasu shugabannin hukumomi su yi ta roko, tabbas ba zan dauki sakaci ba saboda mutuncinmu yana cikin hadari. “.

Sakataren zartarwa ya ci gaba da bayanin cewa jama’a da ma’aikatan hmb ya kamata su sani cewa muna da tsarin tsaro na cikin gida don tantance kwarewar mu na asibiti, sadarwa da kuma da’a na kwararru.

kamar yadda Samira Sulaiman jami ar Hulda da jama a ta hukumar lafiya ta sanyawa hannu

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *