Shugaban Jami’oi Masu Zaman Kansu Na Africa Farfesa Gwarzo Ya Magantu Kan Dakatar da Digirin Benin Da Togo

IMG 20240108 212713

Dole ne mu godewa Allah mu kuma godewa Minisatan ilmin Najeriya bisa kafa kwamatin da ya yi domin nemo bakin zaren Kan badakalar takardun digirin da Jaridar Daily Nagerian ta yi.

Alfijir labarai ta rawaito Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo mamallakin Makarantar Maryam Abacha Maaun da Canadian da Kuma Franko yace babban abinda ya tada musu hankali shine, yadda Makarantar da kanta ce ta mika sunan dalibi dan Jaridar da ya siyi kwalin digiri a sati shida ga hukumar bautar kasa.

Duk da cewar Gwamnatin Catanau din tace bata da masaniyar a kan wannan Digirin.

Gwarzo ya kara da cewar yanzu haka sun kafa kwamati da kansu, kuma nan uku kuma zasu isa can Catanau su zauna da Makarantar domin su ji yadda aka haihu a ragaya.

Farfesa ya ce wannan lamarin suma a kungiyance suna jinsa a jita-jita amma basu taba kamawa ba, amma yanzu wannan dan Jaridar ya tabbatar mana da ana iya yi, Wanda dama mun tabbatar members din mu cewar wannan jita-jitar idan muka samu mutum da ita to lalle ba zamu ci gaba da yadda da amincewa da shi ba, domin zai jefa kungiyar cikin hadari.

Hakazalika a baya ma, mun yi duk mai yiwuwa domin gano hakan abin ya gagara, amma cikin taimakon Allah gashi nan asirin ya tonu. Yanzu haka a matsayinmu na kungiya zamu tsaya mu yi hangen nesa domin fitar da tamu sanarwar da kuma yadda za a magance gaba.

Farfesan yace bayan gwamnatin Najeriya sun kammala nasu binciken muma mun hattama namu to zamu zauna da su a fitar da matsaya, domin laifin mutum daya bai kamata ya shafi kowa da kowa ba.

A kashe Farfesa Gwarzo ya ce yana alfahari da jami oisa guda uku Wajen tsayawa da zage damtse domin yin abinda ya kamata, Kuma duk makircin mai hassada ba zai taba kamamu da irin wannan abin ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *