Shugaban Najeria Tinubu Ya Naɗa Sabbin Shugabannin Hukumar Hajji Ta Kasa

Bola Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin sabuwar hukumar gudanarwa da hukumar alhazai ta kasa (NAHCOM) ya kuma mikawa majalisar dattawan Najeriya domin tabbatar da hakan.

Alfijir labarai ta rawaito Shugaban a cikin kudurinsa na tabbatar da gudanar da aikin Hajji na shekarar 2024 ba tare da matsala ba, ya nada wadannan mutane a Hukumar NAHCOM:

Jalal Arabi- a matsayin Shugaba

  1. Aliu Abdulrazaq – Kwamishina, Siyasa, Ma’aikata, & Kudi
  2. Prince Anofi Elegushi – Kwamishinan Ayyuka
  3. Farfesa Abubakar A. Yagawal – Kwamishinan Tsare-tsare da Bincike

WAKILAN ZONAL

  1. Dr. Muhammad Umaru Ndagi — Arewa ta tsakiya
  2. Abba Jato Kala — Arewa maso Gabas
  3. Sheikh Muhammad Bin Othman — Arewa maso Yamma
  4. Tajudeen Oladejo Abefe – Kudu maso Yamma
  5. Aishat Obi Ahmed — Kudu maso Gabas
  6. Zainab Musa – Kudu maso Kudu
  7. Professor Musa Inuwa Fodio — Jama’atul Nasril Islam
  8. Farfesa Adedimizi Mahfouz Adebola — Majalisar Koli kan Harkokin Addinin Musulunci

Shugaban ya umurci wadanda aka nada su sadaukar da kansu wajen ganin cewa ayyukan hukumar alhazai ta kasa, kuma su kasance masu inganci da gaskiya da kuma biyan bukatun ‘yan Najeriya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *