Shugaban Najeriya Ya Gargaɗi Kungiyar Kwadago kan Zanga-zangar Da Ta Shirya Yi

FB IMG 1706824949754

Daga Aminu Bala Madobi

Gwamnatin Najeriya ta yi kira ga ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar NLC da ta jingine zanga-zangar da ta shirya gudanarwa a faɗin ƙasar ranakun 27 da 28 ga wannan wata, kan tsadar rayuwa.

Alfijir labarai ta rawaito Ministan Shari’a na ƙasar, Lateef Fagbemi, SAN ne ya bayyana gargaɗin cikin wata wasƙa da ya aike wa lauyan ƙungiyar ƙwadagon, Femi Falana ranar Juma’a.

Ministan ya ce “Gwamnati na ƙoƙarin kammala duka batutuwan da ta cimma da ƙungiyar, kuma abin da ya kamata shi ne NLC ta tuntuɓi gwamnati don tabbatar da aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma, musamman a ɓangarorin da matsaloli suka yi katutu”.

Hakazalika ya ƙara da cewa zanga-zangar da ƙungiyar ta shirya gudanarwa ta ci karo da umarnin da kotun da ke hukunta laifukan da suka shafi gwamnati da ƙungiyar ƙwadago.

Lateef ya ce ƙungiyar ta shirya gudanar da zanga-zangar ne saboda zargin gwamnati ta kasa aiwatar da batutuwan da ta cimma da ƙungiyar ƙwadagon ranar 2 ga watan Oktoban bara.

A cikin wasikar ministan ya buƙaci lauyan ƙungiyar ya bai wa ƙungiyar shawarar datakar da zanga-zangar wanda ya ce za ta iya dakatar da ayyukan gwamnati da barazana ga zaman lafiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *