Shugaban Najeriya zai yi jawabi ga ƴan Najeriya dangane da zanga-zanga

FB IMG 1720814344337

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi ga al’ummar ƙasar a wani shirin watsa shirye-shirye a ranar Lahadi, 4 ga watan Agusta, 2024, da karfe 7:00 na safe.

An umurci gidajen Talabijin, Rediyo, da sauran kafafen yaɗa labarai na zamani da su shiga cikin ayyukan sadarwar Hukumar Gidan Talabijin ta Najeriya (NTA) da Hukumar Gidan Rediyon Tarayyar Najeriya (FRCN) don yaɗa shirye-shiryen.

Za a maimaita jawabin a tashoshin NTA da FRCN da karfe 3:00 na rana da 7:00 na yamma duk a gobe lahadi.

Me kuke fatan ji daga shugaban?

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *