Sarki Musulmi Da Obasanjo, sun gargadi Shugabannin kasar nan su daina siyasantar da rashin tsaro a kasar
Best Seller Channel
Best Seller Channel
Dattawan jihohin Najeriya da shugabannin manyan kungiyoyin al’adu a ranar Litinin a Abuja sun yi gargadin cewa shugabannin Najeriya a kowane mataki su daina abin da suka bayyana yadda ake siyasantar da al’amuran da suka shafi tsaron rayuka da dukiyoyi a kasar.
A cewarsu, irin wannan gargadin ya zama dole domin samar da zaman lafiya a Najeriya da kuma daina ta’azzara halin da kasar ke ciki.
The Punch ta rawaito, dattawan jihohin karkashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad da tsohon shugaban
kasa Olusegun Obasanjo, sun yi wannan gargadin ne a lokacin da suke jawabi a wani taron yini daya na ‘Retreat on inclusive security’ wanda gidauniyar Global Peace Foundation ta shirya a gari, hadin gwiwa da Vision Africa.
Best Seller Channel
Sun yi kira ga jiga-jigan da su guji yin tsokaci da za su iya fadada “rashin amana tsakanin yawancin rarrabuwar kawuna” wanda ya kunshi kasar. ‘
Yan majalisar sun ba da shawarar cewa ya kamata a dauki rayuwar Najeriya a matsayin kasa mai tsarki.