Sojoji Sun Kashe Wasu Gawurtattun Ƴan Bindiga Tare Da Kwato Babura 10 A Kaduna

Alfijr ta rawaito Dakarun runduna ta daya ta sojan Najeriya da kuma Air Component na Operation Whirl Punch, sun kashe ‘yan bindiga 5 tare da kwato babura 10 a jihar Kaduna.

Mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta daya, Musa Yahaya ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Kaduna.

Laftanar-kanar, Mista Yahaya, ya ce an gudanar da aikin ne domin samar da yanayi mai kyau na gudanar da babban zabe cikin lumana da samun nasara tare da hana ‘yan bindiga ‘yancin kai dauki a yankin na shiyya ta daya.

“Dakarun runduna ta daya ta sojojin Najeriya da kuma rundunar sojin sama na Operation Whirl Punch sun yi luguden wuta kan ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a jihar Kaduna.

A cikin wani mummunan sintirin fada da ya dauki sama da sa’o’i 48, sojojin sun yi nasarar kwace kauyukan Mando-Sabon Birni-Maidaro-Dogon Dawa, Galadimawa, Saulawa, Farin Ruwa da Polewire a kananan hukumomin Birnin Gwari da Chikun a jihar.

A yayin sintiri, sojoji sun kashe ‘yan bindiga biyar tare da kwato babura 10 daga hannun ‘yan bindigar, yayin da wasu babura da dama suka kone tare da lalata su.

Sauran kayayyakin da sojojin suka kwato sun hada da bindigogi kirar AK 47 guda biyu, na’urorin fashewa guda biyar, wayoyin hannu guda biyu, rigar ‘yan fashi da kuma mujallu.

Mista Yahaya ya ce babban kwamandan rundunar soji ta daya (GOC) ta Najeriya, Manjo-Janar Taoreed Lagbaja ya nuna jin dadinsa da yadda sojojin suka gudanar da aikin tare da yaba musu bisa jajircewarsu.

“GOC ya umarci sojojin da kada su yi kasa a gwiwa har sai an kawo karshen ayyukan ta’addanci, garkuwa da mutane, ta’addanci da sauran laifuka,” in ji Yahaya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *