Sojojin Juyin Mulkin Gabon sun saki Ali Bongo

A ranar 30 ga watan Agusta ne sojoji suka kifar da gwamnatin Ali Bongo bayan da suka yi zargin maguɗin zaɓeImage caption: A ranar 30 ga watan Agusta ne sojoji suka kifar da gwamnatin Ali Bongo bayan da suka yi zargin maguɗin zaɓe

Alfijir Labarai ta rawaito Sojojin da suka yi juyin mulki a Gabon sun bayyana kawo ƙarshen ɗaurin talalar da suke yi wa hamɓararren shugaban ƙasar Ali Bongo, suna masu cewa a yanzu yana da damar barin ƙasar.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin mulkin sojin, Kanal Ulrich Manfoumbi, sojojin suka karanta a gidan talbijin na ƙasar ranar Laraba da maraice, ya ce an saki Ali Bongo ne bisa dalilai na rashin lafiya.

“A yanzu, idan ya ga dama yana iya fita daga ƙasar domin a duba lafiyarsa,” in ji sanarwar.

Tun bayan da sojojin suka kifar da gwamnatin Ali Bongo ranar 30 ga watan Agusta ne suka ci gaba da tsare a gidansa.

Matakin sakin hamɓararren shugaban ƙasar na zuwa ne bayan da sojojin suke ta samun matsin lamba daga ƙungiyar ƙasashen tsakiyar Afirka da ECCAS da kuma maƙwabtan ƙasar na cewa su martaba lafiya tare da mutunta hamɓararren shugaban ƙasar

A shekarar 2018 ne dai, Ali Bongo ya gamu da cutar shanyewar ɓarin jiki.

Yanayin lafiyarsa ya kasance abin damuwa musamman a lokacin yaƙin neman zaɓe.

BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *