Sojojin Nijeriya Sun Sake Hallaka wani Kasurgumin Dan Fashin Daji

Screenshot 20240905 193921 WhatsAppBusiness

Dakarun Nijeriya sun sake samun nasarar hallaka kasurgumin dan fashin daji a Katsina.

Alfijir Labarai ta rawaito wata babbar nasara a yakin da ake yi da ta’ddanci, an kashe kasurgumin dan fashin dajin nan, Sani Wala Burki wanda ke addabar kananan hukumomin Safana da Batsari a jihar Katsina.

Kafar yada labarai mai kawo rahoton tsaro a Arewa, Zagazola Makama ce ta rawaito cewa jami’an tsaro da ‘yan banga na sa kai a jihar Katsina ne suka hallaka dan fashin dajin tare da mayakansa.

Sojojin Nigeria sun Kashe Ƙasurgumin Dan ta’adda da ya addabi Arewacin Nigeria

Lamarin ya faru ne a daren jiya a yayin ‘yan bindigar suka yi yunkurin kai hari ga mazauna garin Safana.

A martanin da suka mayar ‘yan bangar da suka samu hadin kai da jami’an tsaro sun fuskanci ‘yan bindigar.

Acewar mazauna garin, an kashe Burki da mayakansa da dama a yayin fafatawar.

Dole yan Nigeria su dawo daga rakiyar siyasar ubangida wajen zaɓen shugabanni — Shekarau

Sani Wala Burki dai ya shahara wajen kai hare-hare a yankin.

Hakan na zuwa ne bayan sojojin Nijeriya sun kashe kasurgumin dan fashin daji, Kachalla Sububu a jihar Zamfara.

Majiya: Zagazola Makama mai sharhi kan lamuran tsaro a yankin yammancin Afrika.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *