Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce dole ne a dawo daga rakiyar siyasar ubangida domin zaɓen shugabanni nagari.
Alfjir Labarai ta rawaito sanata Shekarau ya kuma yi Allah wadai da yadda wasu ‘yan siyasa ke dakile kwararar romon dimokuradiyya ga ayyukan gwamnati a Nijeriya ta hanyar yin watsi da ƙa’idojin gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyansu.
Shekarau ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da ƙasida mai taken, ƙalubalen gudanar da harkokin siyasa daga jami’an gwamnati’ a wani taro na kwanaki 4 da aka shirya wa mambobin hukumar yi wa ma’aikata hidima ta ƙasa (NASC) da manyan jami’an gudanarwa na majalisar tarayya da aka fara a Abuja ranar Juma’a.
Ibrahim ya ce maganganun da shugabannin siyasa ke yi a bainar jama’a don burge magoya bayansu ya saɓa wa ƙa’idojin aikin gwamnati.
Ya ƙara da cewa, naɗe-naɗen siyasa da ba su da muhimmanci kuma waɗanda ba su zama dole ba, na ƙara yawan kashe kuɗaɗe da hakan yana haifar da ruɗani a ayyukan jama’a.
A cewarsa, batun shugabanci shi ne babban jigon nasara na kowace ƙungiya ko al’umma.
Daily trust
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj.