Sufeto Janar na ‘yansanda, Kayode Egbetokun, ya buƙaci dukkanin ƙungiyoyin da ke shirin gudanar da zanga-zangar a faɗin ƙasar nan da su miƙa bayanansu ga kwamishinonin ‘yansanda a jihohinsu
Alfijir labarai ta ruwaito Egbetokun, wanda ya zanta da manema labarai a shalkwatar rundunar ya ce an gabatar da buƙatar ne don ganin an gudanar da zanga-zangar cikin lumana tare da bayyana cewa bayanan sirri da rundunar ta samu sun nuna cewa sojojin haya na ƙasashen waje na da hannu a zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar.
Da yake amincewa da ‘yancin da kundin tsarin mulkin Nijeriya, ya tanada ga ‘yan ƙasa na damar gudanar da taro ko zanga-zangar lumana, ya bukaci dukan ƙungiyoyin da ke shirya zanga-zangar da su yi wa kwamishinan ‘yansanda cikakken bayani a jiharsu, inda ake son gudanar da zanga-zangar.
Wannan ya ce zai rage hatsarin tashin hankali da lalata dukiya ko wasu ayyukan laifuka daga masu zanga-zangar tare da biyayya ga doka ba take haƙƙin wasu ba, inda ya ce suna sa ido tattare da barazanar zanga-zangar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj