Sulhu Khairan! An Sami Daidaito In Da Sheikh Daurawa ya Amince Zai Koma Bakin Aikinsa

Screenshot 20240305 000052 com.facebook.katana edit 1851727657008


Kwamandan Hisbah ta jihar kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya dawo mukaminsa bayan sulhun da kungiyar Inuwar hadin kan malaman Kano suka jagoranta tsakanin sa da gwamnan jihar kano.

Alfijir labarai ta rawaito a ranar Juma’a data gabata ne Sheikh Daurawa ya bayyana Ajiye mukamin nasa bayan wasu kalamai da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya yi na Kalubalanci yadda hukumar take gudanar da wasu daga cikin aiyukan ta.

Da yake zantawa da Manema labarai Mai magana da yawun gwamnan jihar kano Sanusi Bature Dawakin Tofa yace an sami mahimtar junan ne a wani zama na kimanin tsahon awa guda da akai tsakanin zauren malaman kano da Sheikh Daurawa da kuma gwamna Abba Kabir Yusuf.

” Bayan doguwar tattaunawa duk da ba iya abun da ya faru aka tattauna ba , amma dai an sami daidaito domin Malam yace komai ya wuce kuma zai koma aikin sa ma a gobe talata, domin cigaba da aiyukan da ya saba”. Inji Sanusi Bature

Yace “dama tun da farko a wajen gwamnati Malam bai ajiye aikinsa ba, saboda bai rubuta ba , don haka Ina tabbatar maka da cewa an sami masalaha kuma malam zai cigaba da yin aikinsa yadda ya kama.

A wani rubutaccen jawabi da ya wallafa a sashin shafinsa na Facebook Sheikh Malam Aminu Daurawa ya tabbatar da yin sulhu a dare wannan rana ta litinin.

“ALHAMDU LILLAH
AN SAMI YIN SULHU, ƘARƘASHIN JAGORANCIN INUWAR HAƊIN KAN MALAMAI DA ƘUNGIYOYI,
PROFESSOR BARODO
SHAIK ABDULWAHAB
PROFESSOR SALISU SHEHU
PROFESSOR BABANGIDA
PROFESSOR SA’IDU DUKAWA.
DR MUAZZAM KHALID BUK
DR ENGR BASHIR HANAN
SHAIKH SHEHU MAI HULA
SUKA WAKILCI SAURAN MALAMAI,
ALLAH YA SAKA MUSU DA ALKHAIRI”

“والصلح خير

HISBAH ZA TA CI GABA DA AIKIN TA DARAM BA SANI BA SABO, TARE DA KIYAYE DOKA”. A cewar Daurawa

Wannan batu dai shi ne ya kawo dambarwar da aka kwashe kusan kwana uku zuwa hudu ana yi, wadda ake zargin duk hakan ta farune sakamakon Kamawa tare da gurfanar da Murja Kunya da hukumar Hisbah ta yi a gaban kotu.

FB IMG 1709593298677
Sulhu
FB IMG 1709593303242
Sulhu
Sulhu khairan
Sulhu

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *