Sulhu! Yadda Tinubu Zai Sasanta Tsakanin Kwankwaso Da Ganduje – Jigo A APC

FB IMG 1713288347610

Salihu Lukman, Tsohon Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Ya buƙaci shugaban kasa Bola Tinubu ya sa baki a rikicin siyasar da ke tsakanin Rabiu Kwankwaso, jagoran jam’iyyar NNPP da Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Shugaban jam’iyyar APC na kasa. Lukman ya yi wannan roko ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Yau Talata a Abuja

Alfijir Labarai ta rawaito Salihu ya kuma Buƙaci Shugaban Kasar da ya yi la’akari da tuhume-tuhumen da ake yi na karbar cin hanci da suka kai dala 413,000 da kuma N1.38bn da Gwamnatin jihar Kano ta shigar Game da shugaban jam’iyyar APC na kasa. Dukkansu Ganduje da Kwankwaso, tsoffin gwamnonin Kano, sun kasance abokan juna kafin fadan su saboda sabanin siyasa a jihar.

A jiya ne mai baiwa Gwamna Ganduje shawara kan Harkokin shari’a na gundumarsa dake karamar hukumar Dawakin Tofa a Kano Halliru Gwanzo ya dakatar da shi bisa zargin karbar cin hanci da rashawa. Sai dai kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta kasa da kuma reshen jihar Kano sun yi gaggawar yin Allah wadai tare da karyata dakatarwar, inda suka bayyana cewa Gwanzo da sauran shugabannin jam’iyyar da ke da hannu a ciki ba su da hurumin tsige shugaban jam’iyyar na kasa.

Jam’iyyar APC Ta Zargi Gwamnatin NNPP a jihar Kano wajen kitsa dakatarwar.  Sai dai kuma Lukman ya dage cewa dole ne shugaba Tinubu da manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC su gaggauta shiga tsakani domin sasanta Ganduje da Kwankwaso domin su cigaba da rike madafun iko a Kano da ma fadin Arewa, ko da kuwa ya zama dole a yi sulhu.

Ya kuma jaddada cewa, “A matsayinmu na masu ci gaba, gaskiya ya zama dole, kuma idan aka yi la’akari da yanayin siyasar da muke ciki, dole ne mu yarda cewa Sanata Rabi’u Kwankwaso da jam’iyyarsa ta NNPP suna samun gagarumin goyon baya a jihar Kano. Dole ne mu sake duba batutuwan da suka shafi rashin jituwarsu

“Idan har ana bukatar karin tattaunawa don kawancen siyasa ko hadewa da Kwankwaso da NNPP, ya kamata shugabanninmu su ci gaba da tafiya yadda ya kamata.

Hakazalika shugaba Tinubu da jam’iyyar APC su yi amfani da wannan damar wajen daidaita tushen goyon bayan jam’iyyar.  Wannan ya ba wa Shugaba Tinubu wata dama ta baje kolin ci gabansa da fasaharsa ta siyasa.  Wata dama ce da ake da ita, idan aka yi amfani da ita yadda ya kamata, za ta iya ceto martabar Ganduje a siyasance.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *