Ta Sake Faruwa! Ƴan Bindiga Sun Sake Kashe Sojoji Shida A Jihar Arewa

Screenshot 20240421 083636 Facebook

Rahotanni daga jihar Neja sun bayyana cewa ƴan bindiga sun yi wa sojoji 6 kwanton-bauna a kauyukan Roro, Karaga da Rumace da ke gundumar Bassa a karamar hukumar Shiroro a jihar Neja a daren Juma’a.
An kuma ce an yi garkuwa da wani soja mai muƙamin kaftin a lokacin harin.

Alfijir Labarai ta ruwaito sojojin sun bar sansanoninsu ne a Allawa da Erena domin kai ɗauki bayan an yi musu kiran gaggawa cewa ƴan bindiga sun shiga kauyen Roro.

An kuma ce barayin sun kashe wani mafarauci da wasu manoma biyu tare da kona gidaje, bankunan abinci da kuma babura, kamar yadda wasu mazauna garuruwan su ka shaida wa Daily Trust.

Sai dai kuma rundunar sojin ta yi shiru kan lamarin lokacin da wani wakilin jaridar ya tuntube ta a daren jiya Asabar.

Amma kuma Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Neja, Birgediya-Janar Bello Abdullahi Mohammed, a martani ga sakon da wakilin Daily Trust ya aike masa a jiya, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce “mun hada hannu waje guda ” don gano wa da gurfanar da wadanda suka aikata laifin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *