Ta Sake Faruwa! Kwankwaso Da Tinubu Sun Sake Ganawar Sirri A Abuja

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a zaben 2023 ya sake ziyartar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a Abuja.

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaba Tinubu da Kwankwaso sun gana a ne ranar Alhamis 24 ga watan Agusta, 2023, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Wannan dai na zuwa ne a wasu hotuna da mai taimaka wa Kwankwaso kan harkokin yada labarai, Saifullahi Hassan ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Hassan ya ce shugabannin biyu sun gana ne kan batutuwan da suka shafi kasa.

Ganawar ta zo ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa ‘yan takarar uku na Atiku Abubakar, Rabi’u Kwankwaso, da Peter Obi sun fara tattaunawa kan yiwuwar hadewar, da manufar kafa babbar jam’iyyar da za ta fi kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki.

An tattaro taron shugabannin siyasar guda uku, wanda aka dade ana yi, an fara shi ne da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku da Kwankwaso.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *