Kamfanin dillancin labaran Nijar ANP ya ce ambaliyar ruwa ta kashe mutum 32 cikin watannin baya-bayan nan.
Alfijir Labarai ta rawaito Yankin Tahoua da ke kudancin Æ™asar ne matsalar ta fi Æ™amari, inda mutum 12 suka mutu, sai Maradi mai mutum 10 da Zindir inda mutane shida suka mutu”, kamar yadda ANP ya ruwaito daga ma’aikatar cikin gida ta Æ™asar.
Sai Tileberi mai mutum biyu, da kuma Yamai da Diffa masu mutum É—aiÉ—ai.
Rahoton ya ce mutum tara daga ciki sun mutu ne, bayan da gidajen da suke ciki suka rufta, yayin da 23 suka mutu sakamakon nutsewa a cikin ruwan.
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ake samu cikin takiyar kowace damina, na haifar da ɓarna mai yawa a ƙasar.
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM