Ta’addanci! Kungiyar Gwamnonin Arewa Ta Magantu Kan Harin Garin Mafa

Gwamna Yahya

Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, yayi Alla-wadai da harin baya bayannan da aka kai kauyen Mafa a karamar hukumarTarmuwa a jihar Yobe.

Alfijir Labarai ta rawaito cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labaran gidan gwamnatin jihar Ismaila Misilli, ya fitar a yau Laraba 04, gaSatumba 2024.

Gwamnan ya bayyana harin a matsayin rashin kyautawa wanda ya haifar da tsoro da firgici ga mazauna kauyen.

Gwamnan ya yaba da kokarin da jami’an tsaro suke yi wajen ganin sun dakile ayyukan yan ta’adda, sai da ya bukaci a kara kokari wajen gano wadanda suke da hannu a wannan danyen aiki,” Ina kira ga jami’an tsaro su ribanya kokarin su akan wanda suke yi, kuma wannan abu bai kamata ya tafi a banza ba, dole ne a hukunta duk wanda suke da hannu a lamarin “, acewar Yahya.

Gwamnan ya mika sakon jajantawa na kungiyar gwamnonin Arewa ga gwamnatin Jihar Yobe, da iyalan wadanda lamarin ya shafa, suna masu rokon Allah ya gafarta wa wadanda suka mutu yayin harin, da kuma neman sauki ga wadanda suka jikkata.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

9https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *