Ta’addanci! Yan bindiga sun kashe mutane tara a jahar Filato

A ranar Litinin ne aka tabbatar da mutuwar mutane tara bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Adu da ke gundumar Kwal a karamar hukumar Bassa a jihar Filato.

Kakakin kungiyar ci gaban matasan Miango, Nuhu Bitrus, ya tabbatar da mutuwar mutanen kauyen a garin Jos a ranar Litinin.

“Eh, an kashe mutane tara a jiya (Lahadi) a wani hari da aka kai a kauyen Adu.

Lamarin ya faru da misalin karfe 9 na dare,” in ji Bitrus.

Ya ce harin ya sa al’ummar jihar fasa shirye shiryen bikin cikar Najeriya shekaru 63, maimakon haka, sun mayar da taron da aka shirya yi a ranar Litinin (yau) zuwa ranar makoki da addu’o’i domin kare lafiyar jama’a.

Shugaban matasan ya kara da cewa, “Ba mu ji dadin yadda a yau muke jimamin mutuwar mutanenmu tara a kauyen Adu da aka kashe a daren jiya (Lahadi) a wani hari da aka kai musu ba.

“Abin takaici ne a yayin da wasu ke murnar samun ‘yancin kai na Najeriya karo na 63, mu a nan mun taru ne a Kwal domin binne mutanenmu.

A matsayinmu na al’umma, mun shirya gudanar da bikin murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai a Najeriya karo na 63 a yau (Litinin) da ayyuka da dama amma ba mu kara yin hakan ba.

Mun mayar da taron zuwa ranar addu’a domin kare lafiyar al’ummarmu.”

Shugaban matasan ya yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su daina kai hare-hare a yankunan Bassa.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, Alabo Alfred, ya kasa samun amsa sakon da aka tura masa da wayar da aka tuntube shi domin jin ta bakinsa kan lamarin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *