Takaitaccen Tarihin Marigayi Na’ibin Kano Malam Nazifi Dalhatu

IMG 20240321 WA0003

Daga Abba Tijjani Sulaiman

Malam Nazifi ya fito daga Zuriyar Fulani Mundubawa.

Shi ne Muhammadu Nazifi Dan Limamin Kano Dalhatu Dan Na’ibi Adamu Dan Limamin Kano Muhammadu Dan Limamin Kano Sulaimanu (Limamin Kano na farko a Daular Fulani).

Mahaifiyar sa kuma sunanta Binta ‘yar Limamin Kano Muhammadu Sani ce, Dan Ali Dan Liman Muhammadu. Saboda haka shi ta ko ina Ba Mundube ne.

An haifi Malam Nazifi a shekarar 1942AD (1361 AH) a Unguwar Soron Dinki a cikin Birnin kano.
Ya taso a gidansu a Soron Dinki a gaban Mahaifin sa Limamin Kano Dalhatu (Limamin Kano daga 1956 zuwa 1976). Ya rayu tare da mahaifinsa har sanda ya rasu a 1976.

Malam Nazifi yayi karatun Alqur’ani dana ilimi a wajen Liman Mansur. Bayan yayi karatu sosai sai ya ci gaba da karantarwa a makarantar Allon dake Gidan na su, Gidan da ake kira Gidan Zaure.

Bayan haka kuma a tsarin Aiki na Zamani, Malam Nazifi ya yi aiki a Maaikatar ilimi a matsayin Malami a U.P.E a H.I.S Shahuci, yana koyarwa kuma yana Limanci a Makarantar. Daga bisani kuma da aka bude Sakandare ta Gwammaja l, sai aka maida shi can.

Hakannan kuma ya koyar a Sakandaren yan mata ta Kawaji da kuma Sakandaren K/Nasarawa.

Sannan a cikin shekarar 2001, da aka gina Masallaci a Gidan Sarki na Nasarawa, sai Sarkin Kano Alh Ado Bayero ya nada shi Limamin wannan Masallaci na Gidan Sarki na Nasarawa. Saboda haka shi ne Liman na farko kenan a wannan Masallaci.

A cikin shekarar 2003 aka nada Malam Nazifi a Matsayin Na’ibin kano, bayan rasuwar Na’ibi Malam Aminu. Kuma ya rike wannan matsayi har zuwa ranar Talata 19 ga watan Maris 2024, sanda Allah ya karbe shi.

‘Ya’ yan sa ga su kamar haka:
1) Salihu (Baffa)
2) Hindu
3) Aishatu (Hajiyayye)
4) Sani (Imamu)
5) Adamu
6) Fatima

Allah ya jikan sa ya gafarta masa ya saka masa da alkhairi bisa hidimar sa amin thumma amin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *