Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Alhamis 22/061445AH – 04/01/2024

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Tsohuwar minista Sadiya Umar Farouq ta ki amsa goron gayyatar da hukumar EFCC ta kai mata domin amsa tambayoyi.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani matashi mai shekara 19 da zargin yi wa ‘yar uwarsa ciki a ƙaramar hukumar Tofa da kuma zargin haɗa baki wajen kashe ta.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, ta cafke dan daban da ake zargi da daba wa limamin wuka a unguwar Jakara da ke jihar.

EFCC ta gano wasu makudan biliyoyi da ake nema bayan sun bar asusun gwamnati Hukuma ta tsare wadannan kudi har Naira biliyan 30 a yayin da ake bincike a kan zargin badakalar NSIPA.

Hatsari ya ritsa da ayarin motocin Mataimakin Gwamna Sakkwato, Idris Gobir, inda hakan ya ’yi ajalin wani dan sanda da wani mai daukar hoto a tawagar.

An kama likitar bogi kan zargin kashe mai juna biyu a Kano.

An yi jana’izar limamin masallacin Juma’a da aka harbe a jihar Filato.

‘Yan bindiga sun kashe mutum 6 sannan mutum 1 ya ji rauni sannan sukayi garkuwa da mutane da dama a harin da suka kai a kauyen Nahuce dake karamar hukumar Bungudu dake jihar Zamfara.

Dan bindiga ya harbe limamin wani masallaci a Amurka.

Za a haramta wa Pistorius shan barasa idan an yi masa afuwa.

Iran ta fara makoki bayan harin ta’addancin da ya kashe mutane 103 a Kerma.

Amurka za ta bude iyakokinta da Mexico a wannan Alhamis.

Shugaban Somaliland ya gana da shugaban Masar al-Sisi kan dambarwa da Habasha.

Laliga: Girona ta sami nasara akan Atlentico Madrid da ci 4:3 a wasan jiya.

Laliga: Real Madrid ta sami nasara akan Mallorca da ci 1:0 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *