Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Asabar 02/03/2024CE – 21/08/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Majalisar Wakilai ta bukaci Tinubu ya sake nazarin rahoton Oronsaye kafin aiki da shi.

‘Yan majalisar dokokin jihar Zamfara da aka dakatar sun nemi Shugaban kasa Bola Tinubu ya saka baki a rikicin majalisar.

Babbar Kotun jihar Kano mai zamanta a Ungogo ta bayar da umarnin dakatar da shari’a r da ake yi tsakanin Murja da Hisbah a kotun Musulunci.

Shugaban NLC, Joe Ajaero ya shawarci Tinubu da ya mayar da hankali wajen magance matsalolin kasa maimakon yi wa ‘yan kwadago barazana.

Jaafar Jaafar yace akwai hannun Gwamnan Kano wajen fitar da Murja Kunya daga gidan gyaran hali.

Rigingimun cikin gida na jam’iyyar APC na ƙara tsananta a jihar Benuwai bayan kwace iko da sakatariya, ƴan sanda sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa wasu mambobin APC.

Malam Dikko Radda ya buƙaci gwamnatin tarayya ta taimaka masa a kokarin da yake na kawo karshen ƴan bindiga a jihar Katsina.

Ana zargin talakawa sun saka wawaso a motar BUA da aka ciko ta da katan-katan na taliya a Dogarawa da ke Zariya wani ganau ya shaida cewa ko katan ɗaya ba a bari a cikin motar ba.

Bankin Afirka zai taimaka wa jihar Gombe wajen bunkasa noma da shirye-shiryen inganta rayuwar Jama’a.

An rushe shalkwatar jam’iyyar adawa ta ‘Socialist Party without Borders’, to sai dai sojojin mulkin kasar ba su bayar da wani dalili na matakin ba.

Saudiyya ta gabatar da buƙatar karɓar baƙuncin Kofin Duniya 2034.

Seria A: Ac Milan ta sami nasara akan Lazio da ci 1:0 a wasan jiya.

Bundesliga: Freiburg da Bayern Munich sun tashi 2:2 a wasan jiya.

Lig 1: Monaco da PSG sun tashi 0:0 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *