Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Lahadi 07/09/1445AH – 17/03/2024CE

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta kama wani mutum mai shekara 35 da ake zargi da satar mutane a jihar.

Rundunar Sojin Najeriya ta sha alwashin zakulo bata garin da suka kashe jami’anta 16 da ke aiki da bataliya ta 181 a Karamar Hukumar Bomadi a Jihar Delta.

Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya sanya hannu a kan dokar da ta haramta sayar da burodin da ba a lika takardar shaidar inda ake yin sa ba, tare da jigilar sa a buhu haka kuma an haramta sayar da fetur fiye da lita 50, haka ma an haramta motoci masu gilashi mai duhu a duk fadin Jihar.

Hukumar Kwastam ta mayar wa wasu mutum shida tireloli maƙare da kayan abinci da ta ƙwace a Jihar Katsina.

Kungiyar ACF ta ce bataji dadin dakatar da sanata Ningi da majalisar dattawa ta yi ba.

Gwamnan Kaduna Uba Sani ya ƙaddamar da gina tituna da adadin tsawonsu ya kai kilomita 372 a fadin jihar.

Gwamnatin mulkin soji ta Nijar karkashin Janar Abdourahamane Tchiani ta ce ta soke yarjejeniyar soji da ta kulla da Amurka.

Harin ‘yan ta’adda ya hallaka sojojin Pakistan 7.

EPL: Burnley ta sami nasara akan Brentford da ci 2:1 a wasan jiya.

EPL: Fulham ta sami nasara akan Tottenham da ci 3:0 a wasan jiya.

La Liga: Real Madrid ta sami nasara akan Osasuna da ci 4:2 a wasan jiya.

Bundesliga: Bayern Munich ta sami nasara akan SV Darmstadt da ci 5:2 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *