Daga Baba Usman Gama
Gwamnatin Tarayya tace ta ɗau alwashin ceto mata da kuma ɗalibai da ƴan bindiga suka sace.
Yan majalisun arewacin Najeriya sun zargi Shugaban Majalisar da yi tushe a kasafin kudi.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya faɗa wa BBC cewa 28 daga cikin ɗaliban makarantar Kuriga da ƴan bindiga suka sace sun kuɓuta.
Gwamnatin jihar Sokoto ta ƙaddamar da sabuwar rundunar ƴan sa kai a jihar.
“Ƴan bindiga sun mamaye ɗaruruwan ƙauyuka a arewa inda suka maye gurbin gwamnati da masu sarautun gargajiya. A wannan hali da ake ciki, ba za’a daɗe ba za su soma ƙwace ikon dukkan ƙananan hukumomi,” in ji Audu Bulama Bukarti.
Kwamitin duban wata ya umarci a fara duban watan azumi daga yau Lahadi.
‘Yan bindiga m sun kashe mutane 6 da suka hada da ‘yan sanda hudu a Ebonyi.
Za a kafa cibiyoyi 590 a Jigawa domin ciyar da mutum miliyan 6 abincin azumi a watan Ramadan.
Jam’iyyr a kasar Cote d’Ivoire ta ayyana Laurent Gbagbo ta a matsayin dan takara a saben 2025.
Jam’iyyar RPF mai mulkin Rwanda ta ayyana Paul Kagame a matsayin dan takararta a zaben kasar.
EPL: Arsenal ta sami nasara akan Brentford da ci 2:1 a wasan jiya.
La Liga: Girona ta sami nasara akan Osasuna da ci 2:0 a wasan jiya.
La Liga: Real Soceidad ta sami nasara akan Granada da ci 3:2 a wasan jiya.
Seria A: Inter Milan ta sami nasara akan Bologna da ci 1:0 a wasan jiya.
Bundesliga: Dortmund ta sami nasara akan Werder Bremen da ci 2:1 a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk