Takaitattun Labaran duniya na Safiyar Lahadi 26/11/2023 – 11/05/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Kotu ta bada dama Ajaka da SDP su binciki kayayyakin zaɓen Kogi.

CBN ya umarci bankuna su ƙara narka jarin kuɗaɗe a bankunan su har a kai gejin Dala Tiriliyan 1.

Kotu a birnin kudun jihar Jigawa ta yanke wa Sagir da ke yin lalata da almajirai ta dubura hukuncin ɗaurin rai da rai.

Gogarma Damina ya kwashe sama da mutum 100, bayan an kasa haɗa masa harajin Naira miliyoyin kudin haraji a ƙauyen Matunji a jihar Zamfara.

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ƙaryata zargin cewa shi ne ya ƙaƙaba ɗan cikinsa, Mustapha, a takarar Gwamnan Jihar a zaben 2023.

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya shawarci mutane da su rike Alkur’ani hannu bibbiyu don samun zaman lafiya a kasar.

Isra’ila ta saki fitacciyar Bafalasdiniya Israa Jaabis amma ta hana a yi murna.

An kammala shirye-shiryen gudanar da wasan karshe na dambe a Kano.

Kungiyar Hamas ta ce ta kammala sakin ‘yan kasar Thailand da ta yi garkuwa da su a Gaza saboda sanya bakin da shugaban Turkiyya.

Sojojin Mali sun daƙile wasu hare-haren Alƙa-ida.

Qatar ta ce Hamas ta saki yara takwas da mata biyar ga Isra’ila.

Dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a Landan dan nuna goyon bayan Falasdinawa.

Wolverhampton Wanderers na son aron golan Arsenal Aaron Ramsdale a watan janairu.

EPL: Arsenal ta sami nasara akan Brentford da ci 1:0 a wasan jiya.

Laliga: Atlentico Madrid ta sami nasara akan Mallorca da ci 1:0 a wasan jiya.

Seria A: Milan ta sami nasara akan Fiorentina akan da ci 1:0 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *